in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga kasashen Afrika da su hada kai domin yaki da magunguna marasa inganci
2015-08-12 11:22:44 cri

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta bukaci kasashen Afrika da su hada kai domin yaki da magungunan jabu da marasa inganci.

Hukumar ta WHO ta yi wannan kira ne a yayin shirya wani taron karawa juna sani na shiyya-shiyya na kwanaki uku da ya samu halartar wakilai da dama daga kasashen Afrika, wanda aka fara a ranar talatar nan a birnin Addis Ababa na Kasar Habasha mai taken yadda za'a dakile yawaitar magungunan jabu da marasa inganci.

Da yake jawabi yayin taron, wakilin hukumar WHO dake kasar Habasha Pierre M'Pel ya jaddada bukatar hadin kan kasashen Afrikan a fannin yaki da matsalar yaduwar magungunan marasa inganci a nahiyar.

A cewar Mista M'Pel, an shirya taron ne domin samar da wata kafar tattara bayanai da musayar su da nufin dakile yaduwar magungunan jabu da marasa inganci a tsakainin kasashen dake makwabtaka da juna da ma duniya baki daya.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China