Wannan taro, da zai gudana daga ranar 17 zuwa 19 ga watan Augusta a birnin Kigali, zai janyo hankalin kwararrun sauyin yanayi fiye da 70 da suka fito daga kasashen Afrika, har ma da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da bangaren masu zaman kansu, da za su gabatar da matakan da za a dauki da kuma aiwatar da shirin NAMA.
Makasudin wannan zaman taro shi ne na karfafa amfani da shirin NAMA a matsayin wani matakin aiki domin gudanar da ayyukan da suka shafi sauyin yanayi har zuwa da bayan shekarar 2020. (Maman Ada)