in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Tsakiya: Wani sojin Rwanda ya kashe takwarorinsa hudu na kasar Rwanda dake cikin tawagar MINUSAC
2015-08-09 17:55:49 cri
Wani sojan Rwanda dake cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya ya harba bindiga kan takwarorinsa, a ranar Asabar da safe a birnin Bangui, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutu hudu da jikkata wasu takwas, kafin ya kashe kansa, in ji Joseph Nzabamwita, kakakin jojojin kasar Rwanda a ranar Asabar.

Lamarin ya faru da misalin karfe 5 da mintuna 45 na dare a wani sansanin rukunin sojojin kasar Rwanda. Babu wata masana kan dalilin da ya haddasa wannan kisan kai a halin yanzu. Kuma tuni aka kafa wani kwamitin bincike cikin gaggawa.

Mista Nzabamwita ya kawo maganar ta'addanci, amma kuma ya bayyana cewa akwai yiwuwar matsalar tabin kai.

Sojojin Rwanda dari takwas ne aka jibge a Afrika ta tsakiya tun cikin watan Janairun shekarar 2014, a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Afrika ta Tsakiya (MINUSAC). (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China