in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shinzo Abe bai gabatar da neman afuwa game da laifukan da kasar Japan ta aikata ba
2015-08-14 20:00:02 cri

Firaministan kasar Japan Shinzo Abe, ya yi takarar kalaman neman afuwa da tsaffin shugabannin kasar Japan suka gabatar a baya, sai dai bai bayyana na sa neman afuwa ba, game da laifukan da kasar ta Japan ta aikata yayin yakin duniya na biyu.

Cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniyar na 2, Abe ya sake nanata neman afuwar tsaffin shugabannin kasar, yana mai cewa sun yi nadamar dukkanin munanan laifukan da Japan din ta aikata. Ya ce neman afuwar da tsaffin shugabannin kasar sa suka gabatarwa duniya, za su ci gaba da wanzuwa a tarihi.

A daya hannun kuma firaministan na Japan ya ce ba za a gadarwa zuriyar kasar dake tafe ci gaba da neman afuwa ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China