Shugaban kwamitin IOC Thomas Bach, da ministan harkokin wasanni da tsaron kasar Switzerland Ueli Maurer sun halarci bikin.
A jawabin da ya gabatar Mr. Bach ya bayyana cewa, an kafa tarihi mai yawa, kuma mai muhimmanci, tun bayan da aka kafa cibiyar kwamitin na IOC a birnin Lausanne. Thomas Bach ya kara da cewa, kwamitin IOC da birnin Lausanne sun kiyaye dangantakar musamman a tsakaninsu.
Ya ce tun bayan kafa cibiyar a birnin Lausanne, sauran kungiyoyin wasanni na kasa da kasa, su ma sun fara kafa cibiyoyinsu a birnin. Kuma zuwan kungiyoyin kasa da kasa da dama birnin na Lausanne, ya sa kaimi ga bunkasuwar birnin, har ma da dukkan yanki, da ma dukkan kasar Switzerland.
Kididdiga ta nuna cewa, yawan ma'aikatan kwamitin IOC, da na sauran kungiyoyin wasanni na kasa da kasa dake aiki a birnin ya kai mutum 2150, wanda hakan ya taimaka ga samar da karin guraben aikin yi a kasar.
Kana zuwan masu sha'awar wasanni daga kasashen waje, shi ma ya sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a kasar.
A ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 1915 ne dai Lebaron Pierre De Coubertin, ya tsaida kudurin maida cibiyar kwamitin IOC zuwa birnin Lausanne na kasar Switzerland, daga birnin Paris na kasar Faransa, sakamakon yake-yake da suka kawo babbar illa ga gudanar wasannin Olympics a wancan lokaci. Daga wannan lokaci ne kuma birnin na Lausanne da wasannin Olympics suka kafa dangantakar kawance. (Zainab)