in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ASOIF ta jinjinawa ci gaban da kwamitin wasanni na Olympics na Rio ya samu wajen shirya gasar Olympics
2015-05-05 11:13:19 cri
An gudanar da cikakken zama na kungiyar kula da wasannin gasar wasannin Olympics na lokacin zafi wato ASOIF a birnin Sochi a 'yan kwanakin baya, inda yawancin manyan jami'an kungiyar suka nuna yabo, ga ci gaban da kwamitin wasannin Olympics na Rio de Janeiro ya samu, wajen shirya gasar wasannin Olympics.

A shekarar da ta gabata, a gun cikakken zama na kungiyar ASOIF da aka gudanar a kasar Turkiya, kungiyar ta zargi kwamitin wasannin Olympics na Rio kan aikin shirya gasar wasannin Olympics. A kuma bana shekara an sake gudanar da cikakken zama na kungiyar, inda aka nuna yabo ga kokarin da Rio ya yi wajen shirya gasar wasannin na Olympics.

Shugaban kungiyar ASOIF Ricci Bitti, ya bayyana cewa Rio ya samu babban canji, wajen shirya gasar wasannin Olympics bisa na shekarar da ta gabata, inda aka ci gaba da gina dakunan wasanni yadda ya kamata. Ya ce kwamitin wasannin Olympics na Rio ya yi kokari sosai.

A shekara daya da ta gabata, kwamitin wasannin Olympics na Rio ya gaggauta shirya gasar wasannin Olympics. A kuma farkon shekarar bana, shugaban kwamitin IOC Thomas Bach ya bayyana gamsuwa ga kokarin da kwamitin wasannin Olympics na Rio ya yi. Kana yayin da sashen daidaitawa na kwamitin IOC yake yin bincike karo na 8 ga birnin Rio, ya bayyana cewa, an samu babban ci gaba wajen shirya gasar wasannin Olympics na Rio.

Haka zalika kuma, babban jami'in gudanarwa na kwamitin wasannin na birnin Rio Sydney Levy, ya bayyawa 'yan jarida a kwanakin baya cewa, maganar da mataimakin shugaban kwamitin IOC John Coates ya yi a shekarar bara, cewa aikin shirya gasar wasannin Olympics ta Rio de Janeiro batu ne mafi muni a tarihi dake cike da karin gishiri, wato a matsayin sa ya na ganin an gudanar da aikin shirya gasar yadda ya kamata.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China