in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne Indiya ta nemi karbar bakuncin gasar wasannin Olympics
2015-05-05 11:14:19 cri

Wasu rahotannin baya bayan nan na cewa shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya wato IOC Thomas Bach, zai gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi nan gaba cikin wannan shekara.

Manazarta harkokin wasanni sun bayyana cewa, watakila su tattauna game da bukatar kasar ta Indiya na neman karbar bakuncin gasar wasannin Olympics a karo na farko.

Bayan birnin Beijing na nan kasar Sin da ya dauki bakuncin gasar wasannin Olympics ta shekarar 2008, da kuma birnin Tokyo na kasar Japan, wanda zai gudanar da gasar a karo na biyu a shekarar 2020, a daya hannun ana ganin maiyuwa kasar Indiya ta dauki bakuncin gasar a karo na gaba.

Bisa wasu labarin da aka samu, an ce yayin ganawar da firaminista Modi zai yi da Bach, mai yiwuwa su tattauna kan wannan batu don sauraron ra'ayin kwamitin na IOC.

Wani mamban kwamitin IOC dan kasar Indiya Randhir Singh, ya bayyana cewa shi da abokan aikinsa suna sha'awar ganin kasar Indiya ta dauki bakuncin gasar wasannin Olympics, kana sun za a yi la'akari da kudurin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics din ga kasar a shekarar 2024.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China