A ranar 6 ga watan Janairu na shekarar nan ne shugaban kwamitin neman daukar bakuncin gasar ta Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing, kuma magajin birnin Wang Anshun, ya mika rahoton neman daukan bakuncin gasar ga kwamitin IOC a birnin na Lausanne. Bayan kuma watanni biyu da karbar rahoton ne tawagar bincike ta IOC wadda Alexander Zhukov ke shugabanta, ta kai ziyara birnin Beijing da Zhangjiakou, inda ta gudanar da bincike na tsawon kwanaki 5.
Bisa shirin tawagar, bayan da ta kammala bincike kan Beijing da Zhangjiakou, wato biranen kasar Sin biyu da ke hadin gwiwa wajen daukar bakuncin gasar ta Olympics, tawagar ta bada wasu shawarwari ga Beijing, kana ta rubuta wani rahoton bincike game da birnin ga kwamitin IOC.
Haka zalika tawagar binciken ta IOC ta ziyarci birnin Almaty na kasar Kazakhstan, inda ta nazargi shirin birnin cikin kwanaki 5, wato daga ranar 14 zuwa 18 ga watan Fabarairu, gabanin fara ziyarar ta a birnin Beijing da Zhangjiakou.
A watan Mayun da ya gabata ne kuma tawagar binciken ta mika rahoton ta ga kwamitin na IOC. Kana aka gabatar da abubuwan dake cikin rahoton a ranar 1 ga watan Yunin nan, matakin da zai baiwa biranen biyu dake neman karbar bakuncin gasar ta Olympics damar fahimtar batun jefa kuri'un da za a yi, da tabbatar da wane ne zai dauki bakuncin gasar wasannin na Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022, a yayin cikakken zama na 128, na kwamitin IOC da za a gudanar a ranar 31 ga watan Yuli mai zuwa a kasar Malaysia.
An zayyana cewa, birnin Beijing yana da fifiko a fannoni shida game da daukar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi. Abu na farko, akwai tunanin da birnin Beijing ya gabatar, yayin da yake neman daukar bakuncin gasar wasannin na Olympics, wato batun maida hankali kan 'yan wasa, da samun bunkasuwa mai dorewa, da kuma tsimin kudi wajen gudanar da gasar, kudurorin da suka dace da ra'ayin kwamitin na IOC, a ajandar da ya gabatar ta shekarar 2020 game da wasannin Olympics.
Na biyu, birnin Beijing yana gadaddun wurare da abubuwa na gudanar da wasannin Olympics, kana Zhangjiakou yana da cikakken ikon daukar nauyin gudanar da wasannin kankara. Har ila yau garin Yanqing na birnin Beijing, shi ma yana da ikon gina dakin wasanni mai inganci.
Na uku, idan aka gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a shekarar 2022 a birnin Beijing, za a sa kaimi ga jama'a miliyan 300, a fannin shiga wasannin kankara, wanda hakan zai bunkasa yaduwar wasannin, da samar da matukar gudummawa ga raya sha'anin wasannin Olympics na duniya.
Na hudu, a shekarun baya baya nan, wasannin kankara sun samu karin karbuwa a kasar Sin, inda jama'a da dama ke kara shiga wasannin lokacin sanyi. A halin da ake ciki akwai kungiyoyin 'yan wasan kwallon kankara na matasa 96 a cikin kwaryar birnin Beijing, dake kunshe da yara fiye da dubu 2.
Na biyar, a matsayin sa na babban birni, birnin Beijing yana da karfin karbar 'yan kallo masu yawa. Kuma lokacin da aka gudanar da wasannin Olympics na lokacin zafi a shekarar 2008 a nan birnin Beijing, otel-otel, da kauyen wasannin Olympics, da kafofin watsa labaru, da hanyoyin sufuri, dukkanin su sun biya bukatun masu halartar gasar dama 'yan kallo baki daya, don haka akwai kyakkyawar shaidar samun irin wannan nasar a yayin gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi.
Na shida, birnin Beijing yana da kwarewar gudanar da babbar gasar kasa da kasa, musamman duba da irin kwarewar da ya samu yayin gudanar wasannin Olympics na shekarar 2008, inda aka horar da masana, da kwararru da dama a wannan fanni, wadanda suke da fasahohi masu yawa, matakin da zai taimaka wajen tabbatar da tsimin kudin da za a bukata wajen daukar bakuncin gasar a nan gaba.
Almaty tsohon babban birni ne a kasar Kazakhstan, kuma yanzu haka shi ne babbar cibiyar hada-hadar kudi, kuma birni mafi girma a kasar. Wannan ne kuma karo na uku da birnin Almaty ya nemi daukar bakuncin gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi.
Idan har ya samu izinin gudanar da gasar, hakan zai sa kaimi ga bunkasar wasanni kankara, a yankin tsakiyar nahiyar Asiya, ya kuma baiwa kasar ta Kazakhstan damar kasancewa cibiyar wasanni a wannan yanki. (Zainab)