Makabartan jaruman Sinawan na Rulindo dai kamfanin Sin dake ke gina hanyoyi da gadojin ta bude shi a shekarar 1982, domin binne wani ma'aikacinsa da ya mutu. A shekarar ta 1997 kuma, Mr. Chen Jian wani ma'aikacin nata na daban ya mutu a wajen aiki, don haka sai aka mai da shi jarumi aka kuma rufe shi a wajen.
Tun daga shekarar ta 1982 zuwa 1997 an binne sinawa 10 wadanda suka mutu a lokacin ayyukan sa kai a Rwanda.
Ya zuwa yanzu ayyukan sa kai na sinawa na cigaba da bada taimako ga cigaban kasar Rwanda. Hanyoyi da kamfanonin kasar Sin ke ginawa suna mikawa tazara mai yawa. Sinawan dake kwance a wannan makabarta kuma shaida ne na zumunci dake tsakanin Sin da Rwanda.(Fatimah Jibril)