in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ruwanda ya samu nasarar sake zama shugaban jam'iyyar da ke kan karagar mulkin kasar
2013-12-16 10:42:23 cri

A gun taron wakilan kasa baki daya karo na 12 na Jam'iyyar 'Rwandan Patriotic Front' wato RPF a ran Lahadi 15 ga wata, Shugaban kasar Paul Kagame ya samu nasarar ci gaba da rike mulkinsa a jam'iyyar da ke kan karagar mulkin kasar, wato wato RPF.

Mista Kagame a cikin jawabin da yayi a gun taron yace, Jam'iyyar RPF ta riga ta karfafa matsayinta, don haka yanzu ya bukaci mambobinta da su yi kokari tare da mambobin sauran jam'iyyu, don samar ma kasar ta Ruwanda wata kyakkyawar makoma.

Shugaba Kagame wanda ya lura cewa, ya kamata mambobin jam'iyar RPF su kokarta wajen kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar ya yi kira ga jama'ar kasar da su shiga cikin ayyukan samun bunkasuwar kasa, don canza zaman rayuwarsu.

An kafa Jam'iyyar RPF a watan Disamba na shekara ta 1987, sunanta na da shi ne kawancen dinkuwar kabilun Ruwanda da matasa masu ilmi na kasar wadanda suka yi gudun hijira a Uganda, da Kenya, da Turai suka kafa, a shekara ta 1994, Jam'iyyar RPF ta zama jam'iyyar da ke kan karagar mulki.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China