A cikin 'yan takara 4 dake neman darewa kujerar shugabancin kasar hadda shugaba mai ci Pierre Nkurunziza, wanda kuma shi ne dan takarar jam'iyyar sa ta FDD, yayin da sauran 'yan takara 3 suka fito daga jam'iyyun dake kawance da FDDn, a cewar masu binciken al'amuran siyasa.
Kakakin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ya ce, da fari akwai 'yan takara 8 da suka nuna burin su na shiga zaben, kafin dan takarar babbar jam'iyyar adawar kasar wato Agaton Rwasa, da wasu 'yan takarar 3 sun janye daga shiga zaben, sakamakon zargin da suka yi cewa ba za a yi gaskiya da adalci a yayin zaben ba. (Bako)