in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Museveni ya bayyana kwarin gwiwa game da yiwuwar warware rikicin kasar Burundi
2015-07-16 20:15:03 cri
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ya bayyana kwarin gwiwar sa, game da yiwuwar warware rikicin kasar Burundi cikin lumana.

Mr. Museveni, wanda ke matsayin babban mai shiga tsakani a rikicin na Burundi, ya fidda wata sanarwa dake cewa tsagin gwamnati, da na 'yan adawa, tare da sauran jam'iyyun gama kai a Burundi, sun amince su koma teburin shawarwari, da nufin kawo karshen rashin fahimtar juna dake haifar da tsahe-tashen hankula a kasar.

Sanarwar ta ranar Laraba, ta ce sassa masu ruwa da tsakin sun kuma amince su gudanar da tattaunawa ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Shugaba Musaveni wanda ke ziyayar aiki ta yini biyu a Burundi, ya kara da cewa a Alhamis din nan ne ake sa ran isar ministan tsaron kasar sa Crispus Kiyonga kasar Burundi, duka dai karkashin manufar shiga tsakani, wadda shugabannin kungiyar kasashen gabashin Afirka suka gabatar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China