Sanarwar ta bayyana cewa, Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Burundi da su nuna sanin ya kamata, su shiga shawarwarin siyasa, tare da sanya moriyar kasar gaba da komai. Ya ce MDD za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da kungiyar kasashen gabashin Afirka ta EAC, da kungiyar AU, domin lalubo hanyoyin warware matsalar kasar Burundi.
Sanarwar ta kara da cewa, Ban Ki-moon ya yi maraba da kokarin kungiyar AU na tura masu sa ido da masana a fannin aikin soja zuwa kasar Burundi, don taimakawa kasar wajen magance tsanantar rikici, da nemo hanyar warware rikicin siyasar kasar cikin lumana. (Zainab)