in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda ya kai ziyara kasar Burundi a kokarin daidaita rikicin siyasa
2015-07-14 19:25:04 cri
A yau Talata 14 ga watan ne shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni, ya kai ziyara kasar Burundi a madadin kungiyar tarayyar kasashen gabashin Afirka ta (EAC), a wani yunkuri na kawo karshen rikicin siyasan dake addabar kasar ta Burundi.

Fadar shugaban kasar Uganda ta fidda sanarwa a wannan rana, wadda ke cewa shugaba Museveni zai gana da jami'an gwamnatin Burundi, da kuma wakilan jam'iyyar adawar kasar.

A ranar 31 ga watan Mayun bana ne dai shugabannin kasashe membobin kungiyar EAC, suka gudanar da taron koli kan batun Burundi a birnin Dar es Salaam, inda aka tabbatar da Mr. Museveni a matsayin wanda zai kasance mai shiga tsakani, tsakanin gwamnatin Burundin da bangaren jam'iyya mai adawa da gwamnatin kasar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China