in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarzoma ta barke a hedkwatar Senegal
2015-06-14 13:54:04 cri
A jiya Asabar 13 ga wata, a kasuwar Petersen dake birnin Dakar, hedkwatar kasar Senegal, tarzoma ta barke tsakanin mazauna da 'yan sanda a yunkurin gwamnati na wargaza gine gine, inda masu boren suka cunna wuta ga kantuna da dama.

Wakilinmu ya samu labarin daga wurin cewa, a safiyar ranar, gwamnatin birnin Dakar ta gudanar da aikin wargaza gine gine dake kasuwar Petersen, amma masu kantunan sun nuna adawa sosai, daga bisani bangarorin biyu sun shiga tarzoma, tare da cunna wuta a wurin. Ganin cewa yawancin shagunan na katakai ne ya sanya wutar ta bazu cikin sauri, har ma kantuna da yawa sun kone kurmus. Kawo yanzu dai, an shawo kan gobarar kuma babu wani mutumin da ya mutu sakamakon wannan rikici.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China