Yu ya ce, Sin tana dora muhimmanci sosai kan bunkasa dangantaka tsakaninta da Senegal, kuma ta nuna mata goyon baya a kokarinta na raya manyan ayyuka masu amfanin jama'a, da raya tattalin arziki, da kyautata rayuwar jama'a. Majalisar CPPCC na fatan karfafa hadin gwiwa da sada zumunci tsakaninta da majalisar dokoki da sauran sassan kasar Senegal, tare da kara yin mu'amala da hadin gwiwa tsakaninta da majalisar kula da tattalin arziki, da zaman al'umma, da kuma muhallin kasar, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasa dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.
A nata bangare kuma, madam Tall ta bayyana cewa, Senegal ta nuna yabo ga manufar da Sin take bi a fannin yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, kuma tana fatan karfafa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, tare da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki, cinikayya, da kuma zuba jari.(Fatima)