Ministan Ndiaye ya fadi hakan ne, a jiya Alhamis yayin da yake duba aikin gina gidan nune-nunen da gwamnatin Sin ke ginawa
Gidan yana cikin birnin Dakar hedkwatar kasar Senegal, kuma yana kusa da babban dakin wasan kwaikwayon kasar da Sin ta taimaka wajen ginawa. A watan Disamba na shekarar 2013 ne, aka fara aikin gina wannan daki, kuma an kimanta cewa, za a kammala aikin gine-gine don fara amfani da shi wajen nune-nunen kayayyakin fasahohi na bakaken fata a watan Afrila na shekarar 2016.
Bayan da wakiliyar kungiyar UNESCO a yankin yammacin Afrika Saidou Sireh Jallow Ann Therese Ndong-Jatta ta ziyarci wurin, ta ce, gidan nune-nune da Sin ta gina ya cimma burin al'ummar Senegal zuriya bayan zuriya, kuma ya samar da wani dandali wajen nuna wayewar kan bakaken fata a duniya, lamarin da ke da ma'anar musamman wajen sa kaimi ga musayar al'adu da yada akidar zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya.
Jakadan Sin a Senegal Xia Huang ya ce, yayin da firaministan Sin Li Keqiang ya ziyarci Afrika a bara, ya ce, ya zama dole a raya tattalin arziki da cinikayya, da al'adu bai daya, don bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Afrika yadda ya kamata, dakin wasan kwaikwayo da gidan nune-nunen wayewin kan bakaken fata sun kasance muhimman nasarorin da aka samu ta hanyar hadin gwiwar al'adu a tsakanin kasashen biyu.(Bako)