A cikin wata sanarwa ta fadar shugaban kasar da aka fitar a birinin Kampala, mista Kiir ya bayyana godiyarsa ga takwaransa na Uganda Yoweri Museveni har zuwa ga sojojin tsaron kasar Uganda, dake ceton rayukan fararen hula da dukiyoyin jama'a da watakila da an rasa su sakamakon yakin.
"Na sani cewa wannan ba ya cikin jadawalin taro amma ina son tabo wannan magana a nan. In ba da sanya hannun shugaba Museveni ba, da an yi asarar rayuka da dukiyoyin jama'a. Kuma duk da haka mun lashi takobin murkushe abokin gaba inda ya ci gaba da take yarjejeniyar tsagaita bude wuta," in ji mista Kiir.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu, ya yi wadannan kalamai a yayin bude dandalin shirin dunkulewar yankin Couloir Nord a hotel din Serena dake Kigali, babban birnin Rwanda.
Mista Museveni ya aike a karshen watan Disamba da wata tawagar ma'aikatan sojoji da jiragen yaki domin dakatar da abin da ya kimanta da shirin kisan kiyashi a Sudan ta Kudu. (Maman Ada)