in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta taimaka wa Kenya a fagen 'yaki da ta'addanci
2015-05-05 09:55:18 cri
Ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a kasar Kenya, ya bayyana a birnin Nairobi na Kenya cewa, kasar Amurka za ta taimaka wa gwamnatin kasar Kenya a fagen yaki da ta'addanci, harkar tsaron kasa da kuma batun 'yan gudun hijira, haka kuma, ya ce, ziyararsa zuwa kasar Kenya a wannan karo share fage ne kan ziyarar aikin da shugaban kasarsa Barack Obama zai kai kasar Kenya a watan Yuli.

Bugu da kari, a yayin taron maneman labaran da aka yi a wannan rana, John Kerry ya bayyana cewa, kasar Amurka za ta samar wa kasar Kenya dallar Amurka miliyan dari daya domin yaki da ta'addanci, kuma za ta samar wa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD dallar Amurka miliyan 45 domin taimaka mata wajen warware matsalar da 'yan gudun hijira ke fuskanta a kasar Kenya.

A wani ci gaba kuma, Kerry ya ce, kasar Amurka tana fatan kasar Kenya za ta ci gaba da bude sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da kuma ba da kariya ga sojojin kasar Amurka dake kasar ta Kenya. Ya ce, gwamnatin kasar Amurka za ta ci gaba da nuna goyon baya ga tawagar musamman da kungiyar AU ta tura zuwa kasar Somaliya domin yaki da kungiyar Al-Shabaab, da kuma ba da taimako wajen farfado da tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar Somaliya.

A baya, mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ya bukaci a rufe sansanin 'yan gudun hijira dake Dadaab, bisa zargin cewar, 'yan gudun hijira na kasar Somaliya dake zama a sansanin suna kawo barazana ga tsaron kasar Kenya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China