in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya zata yi wa mutane 86 da ake zargi da alaka da ta'addanci tambayoyi
2015-04-11 17:24:18 cri
Hukumomin kasar Kenya sun bukaci a ranar Jumma'a mutane da kungiyoyi 86, da aka rufe asusunsu a bankuna bisa zargin cewa suna taimakawa ta'addanci, da su bayyana gaban cibiyar yaki da ta'addanci a mako mai zuwa domin su amsa tambayoyi.

Sufeto janar din 'yan sanda, Joseph Boinet ya bayyana cewa wadannan mutane da ake zargi da hannu a cikin ayyukan kungiyar Al- Shabaab zasu bayyana gaban cibiyar samar da bayanai kan yaki da ta'addanci domin su kare kansu da alaka da wadannan kungiyoyi.

Cibiyar samar da bayanai ta kasa kan yaki da ta'addanci nada sansaninta a birnin Nairobi, kuma mutanen da ake zargi da hada kai da kungiyar Al-Shabaab zasu bayyana domin suna nuna cewa basu cikin mutanen da ake zargi, in ji mista Boinet.

An fitar da wannan takardar jerin sunayen mutane bayan harin ta'addancin garin Garissa dake arewa maso gabashin Kenya, inda mayakan kungiyar Al-Shabaab suka kashe mutane 148.

Gwamantin Kenya ta sanya kungiyar Al-Shabaab a cikin jerin kungiyoyin ta'addanci, daidai da Boko Haram, Kungiyar IS da sauransu.

Haka kuma, Kenya ta dakartar da lasin wasu kamfanonin aiken kudi goma sha uku da take zarginsu da tallafawa ta'addanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China