A cikin sanarwar na ta mujallar gwamnati, an kuma bada umurnin ga duk bankuna dabankunan kananan masana'antu da kada su gudanar da huldarsu da wadanda aka lissafa ta tare da bada bayanai na duk wani wata mu'amala da aka yi da su ga babban bankin kasar cikin awowi 48.
Sakataren baitul malin kasar Kamau Thugge ya shaida ma manema labarai a Nairobi cewa gwamnati ta kuma dakatar da duk wani nau'in musayar kudi da alummar Somaliya.
Jerin sunayen dai yazo ne sakamakon harin da aka kai ga jami'ar Moi na garin Garissa a ranar alhamis din makon jiya inda aka hallaka mutane 148 sannan wassu sama da 70 suka ji rauni.
Wannan sanarwar gwamnatin da ya fara aiki tun daga ranar talata 7 ga wata ya lissafa sunayen kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da Al shabaab, Boko Haram, IS na Iraqi da kuma ISIS na Sham sannan da MRC na Mombasa.
Sakataren jamalissar tsaron kasar Raychelle Omamo yace gwamnati ta riga ta dauki matakan kakkabe ta'addanci a doron kasar Kenya.(Fatimah Jibril)