Kaza lika ofishin ya rawaito manzon musamman na babban magatakardan MDD kan batun Syria Steffan de Mistura, na cewa za a gayyaci bangaren gwamnatin kasar Syria, da wakilan kungiyoyin 'yan adawa, da kuma wakilan jama'ar kasar ta Syria, da ma wasu wakilan shiyya-shiyya da na kasa da kasa wadanda abin ya shafa, inda za su tattauna yanayin da kasar ke ciki a halin yanzu.
Har wa yau ana fatan gabatar da shawarwari game da yadda za a iya aiwatar da kudurorin dake kunshe cikin yarjejeniyar Geneva kan batun kasar ta Syria da aka kulla a baya.
Bugu da kari, rahoton ofishin ya ce, za a gudanar da shawarwarin na wannan zagaya a asirce, kana ba za a fidda sanarwar kafin, ko bayan kammalar taron ba. Sai dai bayan kammalarsa, Mr. Mistura zai gabatar da sakamakon shawarwarin da aka cimma ga babban magatakardan MDD. (Maryam)