Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Syria ya ruwaito sanarwar ma'aikatar harkokin wajen kasar na cewa, shawarwarin da aka yi tsakanin gwamnati da kungiyar adawa ta kasar Syria a birnin Moscow na kasar Rasha, shi ne wani matakin farko na fara shawarwari, inda ana sa ran bayan shawarwarin, za a iya fara shirya shawarwarin kasar Syria na ita kanta, wanda babu kasashen ketare da za su tsoma baki a ciki ba. Kuma gwamnatin kasar Syria na maraba da yin shawarwari tare da duk wanda ke son goyon bayan kasar wajen kiyaye hadin kan al'ummominta, 'yancin kanta, ikon mulkinta da kuma cikakken yankunanta.
Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Alexander Lukashevich ya bayyana a ran 25 ga wata cewa, kasarsa na son ba da wata dama ga gwamnatin kasar Syria da kungiyar adawa ta kasar domin su gana da juna a babban birnin kasar, Moscow da kuma yin kwarya-kwaryan shawarwari a tsakaninsu. (Maryam)