Reshen kungiyar Al-Qaida ya yi garkuwa da fararen hula kimanin dari 3 a kasar Syria
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Syria suka bayar, an ce, reshen kungiyar Al-Qaida wato kungiyar Al-Nusra ta yi garkuwa da fararen hula Kurdawa kimanin dari 3 a jihar Idleb dake arewacin kasar Syria a ranar 6 ga wata, ciki har da mata da kananan yara da dama. Ya zuwa yanzu dai kungiyar Al-Nusra ta riga ta tura keyar wadannan fararen hula zuwa kotunan addini dake wurin.
Kungiyar Al-Nusra mai matukar karfi ta fuskar soja dai reshen kungiyar Al-Qaida ce a kasar Syria, dake gudanar da ayyukanta a fagen daga na Syria da kuma karfin fada a ji ta fuskar aikin soja. Kungiyar Al-Nusra da kungiyar IS sun taba yi hadinhadin kansu wajen gwiwa domin mamaye sansanin 'yan gudun hijira na Yarmuk dake kusa da birnin Damascus a ranar 1 ga wannan wata, lamarin da yanzu ya kasance wata babbar barazana ga tsaron birnin Damascus. (Zainab)