Ali Larijani dake ziyara a kasar Lebanon ya gana da shugaban majalisar dokokin jama'ar kasar Nabih Barri da firaministan kasar Tammam Salam, bayan haka ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, kasarsa tana fatan za a warware rikicin na Syria ta hanyar siyasa.
Ya ce, bai kamata a yi amfani da karfin tuwo don cimma burin kafa mulkin demokuradiyya ba, kana yadda wasu kasashen yammacin duniya da kasashen dake dab da kasar Syria suka tsoma baki kan batun kasar, ya haddasa bullar 'yan ta'adda a yankin.
Ban da wannan kuma, Larijani ya bayyana cewa, Iran da Amurka ba su cimma daidaito kan batun yaki da ta'addanci ba. (Zainab)