Bugu da kari taron da aka bude yau a birnin Malabo, fadar mulkin Equatorial Guinea zai kuma tattauna yadda kasashen da cutar ta fi yi wa illa ke farfadowa.
Taron na yini biyu mai taken "taimakawa kasashen Afirka wajen farfadowa tare da sake gina kasa bayan cutar ta Ebola" zai kuma hallara kan jami'an gwamnatoci, hukumomin MDD da na shiyya-shiyya, da kuma sassa masu zaman kansu, inda ake sa ran za su kara yin musayar ra'ayoyi game da irin darussan da aka koya a yaki da cutar Ebola.
Ana kuma sa ran taimakawa kasashen da cutar ta fi yi wa ta'adi, musamman kasashen Guinea, Liberia da Saliyo ta yadda za su farfado da kuma kara matakan kantagarkin barkewar cutar a nahiyar. (Ibrahim Yaya)