Mr. Jin ya kara da cewa baya ga kasancewar cutar Ebola barazana ga kasashen Afrika, a hannu guda ta haifar da wata dama ta inganta kiwon lafiya a kasashen Afrika.
Ya ce bayan barkewar cutar, kasar Sin ta samar da tallafi a fannin kiwon lafiya da ba a taba ganin irinsa ba, ta kuma samar da kudin agajin da yawansa ya kai sama da dalar Amurka miliyan 120 cikin matakai 4 ga wasu kasashe da yankuna 13 da bala'in ya shafa. Kaza lika Sin ta tura likitoci sama da 1200 zuwa wuraren da wannan annoba ta bulla. Har wa yau gwamnatin Sin ta dora mihummanci game da taimakawa kasashen da bala'in ya shafa, ta hanyar inganta harkar kiwon lafiyar su, ta kuma shugabanci aikin taimakawa kasashen Afrika wajen yaki da cutar Ebola, kuma ta samu babban yabo daga nahiyar Afrika, da ma sauran kasashen duniya baki daya.
Mr. Jin ya ce, kasar Sin za ta yi kokari tare da kasashen duniya, wajen ba da tallafi ga kasashen Afrika bisa bukatunsu, bayan da aka shawo kan cutar, kana za ta goyi bayan aikin kafa tsarin kandagarki a nahiyar Afrika, da gina muhimman ababen more rayuwa a fannin kiwon lafiya, don daidaita matsalolin ba zata. (Bako)