Jami'ar Oxford ta bayyana cewa, manazarta suna shirin neman masu aikin sa kai sama da 600 a Birtaniya da Faransa, wadanda ke da lafiya, domin shiga wannan aikin gwajin allurar. Bayan haka, za a gudanar da gwajin allurar a kasashen yammacin Afirka da cutar Ebola ke fi yaduwa.
A cikin mataki na farko da aka yi, an yi gwajin allurar ga masu aikin sa kai na Birtaniya 87. Sakamakon da aka samu ya nuna cewa, allurar na da amfani, kuma babu wata illar mai tsanani da ta kawo wa jikin mutanen da aka gwajin kansu.(Fatima)