Aikin da ke jiran mu mai girma ne: ya kamata mu tabbatar da alkawuran da muka dauka na bada taimakon hadin gwiwa, in ji mista Ban a cikin wani jawabin bude wannan taron, a gaban idon shugabannin kasashen Guinee, Laberiya da Saliyo.
Hadin gwiwar shiyyar ya kasance wani muhimmin mataki domin sanya ido ga annobar kuma zai kasance muhimmin aiki domin tabbatar da samun galaba kan wannan cuta yadda ya kamata, in ji Ban Ki-moon, tare kuma da yabawa ma'aikatan sa kai na Afrika 800 da aka tura bisa tsarin taimaka wa kungiyar tarayyar Afrika AU wajen fuskantar annobar.
Sakatare-janar na MDD ya kuma nuna yabo ga kasahen da suka amsa kiran bada taimako a lokacin da annobar ke tsanani, lamarin da ya taimaka wajen dakatar da yaduwar cutar ta hanyar taimakon kayayyaki da magunguna. (Maman Ada)