A ranar Alhamis ne aka bude wata tattaunawa game da zakulo matakan da za a bi, wajen farfadowar kasashen nan uku dake yammacin Afirka, wadanda suka fi fuskantar matsalar yaduwar cutar Ebola.
A cewar kakakin MDD Stephane Dujarric, taron ya gudana ne karkashin jagorancin kasashen uku, wato Guinea, da Laberia da kuma Saliyo, ya kuma zo a daidai gabar da sassan masu ruwa da tsaki ke shirin bude babban taron tattaunawa a Juma'ar nan, don gane da tallafawa kasashen uku da hanyoyin shawo kan wannan matsala.
Dujarric wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru, ya bayyana cewa, ana sa ran ministocin kudaden kasashen uku, za su gabatar da tsare-tsaren kasashensu na tsahon shekaru 2, game da matakan farfadowa.
Ana kuma fatan wakilin musamman na babban magatakardar MDD David Nabarro, da manzon musamman na MDD game da cutar Ebola Sunil Saigal, tare da wasu jami'an hukumar UNDP ta MDD, za su gana da 'yan jaridu bayan taron na yau Juma'a.
Cikin manyan jami'ai da za su halarci wani bangare na ganawar da za a yi a helkwatar MDD, hadda babban magatakardar majalissar Ban Ki-moon, da shugabannin kasashen uku, da kuma wakilai daga kungiyar AU. Sauran sun hada da wakilan bankin raya Afirka, da na tarayyar Turai, da na bankin musulunci na IDB, tare da sauran sassan masu ruwa da tsaki.
Ana dai fatan wannan taro zai ba da damar samar da taimako, da kwarin gwiwa ga kasashen da Ebola ta yiwa ta'annati. (Saminu)