in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Cote d'Ivoire: Kasar Sin ta zama abar koyi ga kasashe masu tasowa
2015-07-17 14:03:00 cri

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, ya ce kasar Sin ta kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, ta yadda ta zama abar koyi ga kasashen masu tasowa, a sa'i daya kuma Sin din ta zamo kyakkyawar kawa ga Cote d'Ivoire.

Mr. Ouattara wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, lokacin da yake karbar takardar kama aiki daga sabon jakadan kasar Sin a Cote d'Ivoire Tang Weibin, ya ce yana fatan zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasar sa da Sin a dukkan fannoni. Ya kara da cewa yana fatan sabon jakadan na Sin, zai kara inganta huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, Tang Weibin cewa ya yi gwamnatocin kasar Sin da kasashen Afrika, na kokarin karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, kuma yana fatan kara ingnata amincewa da juna a fannin siyasa, da nuna goyon baya ga juna tare da gwamnatin Cote d'Ivoire, domin habaka hadin gwiwar kasasashen biyu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China