Wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD mai kula da harkokin Cote d'Ivoire, madam Aichatou Mindaoudou ta yaba wa kokarin da jam'iyyu daban daban na kasar suke yi wajen inganta yunkurin babban zabe a jiya Laraba.
A wannan rana a Abidjan, babban birnin kasar, a gun wani taron musayar ra'ayi da aka yi a tsakanin tawagar dake kula da harkokin Cote d'Ivoire ta MDD da matasan jam'iyyun kasar, Aichatou Mindaoudou ta nuna cewa, tawagar za ta yi iyakacin kokarin wajen taimakawa hukumar zaben kasar.
Cote d'Ivoire za ta yi babban zabe a watan Oktoba na wannan shekara, domin kaucewa irin rikicin zaben da ya faru a bayan babban zabe na shekarar 2010, membobi 17 da suka fito daga jam'iyyu da bangarori daban daban na kwamitin zabe mai zaman kansa sun yi rantsuwar aiki a ranar 11 ga watan Agusta na shekarar bara.(Lami)