A wannan rana, a birnin Tengréla dake yankin arewacin kasar, mai nisan kilomita 800 daga hedkwatar kasuwancin kasar wato Abidjan, firaministan Duncan ya nuna godiya ga kamfanin gine-ginen. Ya ce, hanya mai lamba 130 da aka kammala ta, ko da yake, an yi fama da yake-yake yayin da aka gina ta, amma masu aikin gine-ginen sun aiwatar da kwangilar yadda ya kamata, sun kuma kammala gina hanyar mai lamba 130 mai inganci kuma cikin lokaci. Ya kara da cewa, yana da tabbaci sosai game da aiwatar da kwangilar a tsakanin bangarorin 2, da kafuwar sabuwar hanyar da za a fara ginawa, kuma ya yi imani da cewa, nan da shekara guda, za a mika wata hanya mai kyau gare su.
Bisa labarin da manajan kamfanin COHL Hu Tao ya bayar, an ce, wannan hanya ta tashi daga birnin Bolona dake yankin arewacin kasar, zuwa birnin Tengréla, sannan ta dire a iyakar kasar Mali, sannan tsawonta ya kai kilomita 43, tare da kasancewa wata babbar hanya a kasar Cote d'Ivoire wadda ta hada wassu kasashen kungiyar ECOWAS.(Bako)