Yayin ganawar tasu, Mr. Chang ya ce tun bayan kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da kasar Cote d'Ivoire, sassan biyu ke ci gaba da raya alakarsu cikin kyakkyawan yanayi. Ya ce, rundunar sojojin Sin na dora muhimmanci sosai game da zumuncin da ke tsakaninsu da takwarorinsu na kasar Cote d'Ivoire, kana suna fatan ci gaba da kokari tare da Cote d'Ivoire, wajen inganta ziyarar manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu, da mu'amalar jama'a tsakanin kasashen biyu, da yalwata hakikanin hadin gwiwar sojojin kasashen biyu, don daukaka zumunci a tsakanin sojojinsu.
A nasa bangare, Mr. Koffi ya ce, Sin sahihiyar abokiyar hulda ce ga Cote d'Ivoire. Kuma rundunar sojojin kasar na fatan kyautata huldar dake tsakaninsu, gami da karfafa hadin gwiwarsu a fannonin horar da ma'aikata da dai sauransu.
Kafin ganawar tasu dai, sai da Mr. Chang ya shirya bikin maraba da ziyarar Koffi a kasar Sin, kana ya zagaya da shi don kallon faretin sojojin ruwa, da na kasa, da sama na kasar Sin.(Bako)