in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan gudun hijirar Cote d''Ivoire sama da dubu 40 ne ke ci gaba da zama a Liberia, in ji hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD
2014-04-01 16:51:15 cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce, kashi biyu bisa uku na 'yan gudun hijirar kasar Cote d''Ivoire da ke zaune a kasar Liberia sun koma kasarsu, yayin da kimanin mutane dubu 46 ke ci gaba da zama a kasar ta Liberia.

Wakilin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD dake kasar Cote d''Ivoire Mohamed Toure ya bayyana cewa, a halin yanzu, hukumar na dukufa wajen dawo da 'yan gudun hijirar, wadanda ke son komawa Cote d''Ivoiren. Kuma bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan 'yan gudun hijirar da suka riga suka koma gida daga Liberian ya kai dubu 20 a ko wace shekara. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China