Kuma bisa kundin tsarin mulkin kasar Lebanon, majalisar dokokin kasar ce ke zabar shugaban kasar, amma sai an samu kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar kafin majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar zaben shugaban kasar.
Adadin 'yan majalisar dokokin kasar na wannan karo guda 128 ne, amma adadin 'yan majalisar da suka kada kuri'u a ran 15 ga wata 46 ne kawai, don haka bai kai adadin da kundin tsarin mulkin kasar ya tsara ba. (Maryam)