in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Lebanon ya yi kira da a tsara shirin taimakawa 'yan gudun hijirar kasar Syria
2014-12-16 16:01:53 cri
Firaministan kasar Lebanon Tammam Salam ya yi kira da a tsara shirin taimakawa 'yan gudun hijira na kasar Syria.

Salam wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin a birnin Beirut, yayin taron tsara shirin taimakawa 'yan gudun hijirar da kasar Lebanon ta shirya a wannan rana, ya ce a halin yanzu 'yan gudun hijirar kasar ta Syria da dama sun shiga kasar ta Lebanon, matakin da ya haifar da illa ga tattalin arziki da ayyukan more rayuwa da hidimar zamantakewar al'umma a kasar Lebanon.

Kana yawan kudin da ake bukata wajen tsugunar da 'yan gudun hijirar ya haura yawan kudin gudummawa da kasar Lebanon ta samu, kana hukumar shirin hatsi ta duniya ta MDD, ta tsaida kudurin dakatar da samar da hatsi ga 'yan gudun hijirar na Syria, wanda hakan ya tsananta halin da ake ciki.

Salam ya bayyana cewa, kasar Lebanon tana fatan za a tsara wani shiri na samar da sauki ga kasashe masu bada gudummawa, da su samar da cikakken kudi, don biyan bukatun wannan fanni. Kana yana fatan kasashe masu samar da gudummawar za su dage wajen tallafawa kasashen da suke tsugunar da 'yan gudun hijirar kasar ta Syria, yayin da suke bada gudummawar jin kai ga 'yan gudun hijirar, don taimakawa kasashen wajen samun bunkasuwa mai dorewa.

A nasa bangare mataimakin babban sakataren MDD Jan Eliasson, ya bayyana cewa, MDDr ta fahimci irin matsin lambar da kasar Lebanon ke fuskanta, kuma MDD za ta ci gaba da samar da gudummawa ga kasar Lebanon. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China