Nasrallah ya bayyana hakan ne a shirin wani gidan telabijin na kungiyar Hezbollah, inda ya ce kungiyar ba ta da ra'ayin nuna hamayya yayin da take neman shiga cikin sabuwar gwamnatin. Maimakon haka, tana son samun damar hadin kai, da samun masalaha, da yin mu'amala a tsakanin bangarorin kasar daban daban, a kokarin magance cacar baki, wanda a cewarsa ya dace da moriyar dukkan bangarorin. Sa'an nan, mista Nasrallah ya nuna fatansa na ganin sabuwar gwamnatin za ta yi kokarin dakile duk wani nau'in aikin ta'addanci, da warware matsalolin da kasar ke fuskanta a fannonin tattalin arziki da zaman takewar al'umma.
Kafin haka, shugaban kasar Lebanon Michel Suleiman ya sanar da kafuwar sabuwar gwamnatin kasar karkashin jagorancin firaminista Tammam Salam a ranar 15 ga wata, lamarin da ya kawo karshen halin kiki-kaka a fannin siyasar kasar wanda aka yi watanni 10 ana fama da shi. (Bello Wang)