Sanarwar ta ce, harin da aka kai a ranar 2 ga wata ya haddasa mutuwar sojoji a kalla 14, tare da jikkata wasu 86 kana 22 suka bace, baya ga fararen hula da suka mutu ko suka ji rauni.
Kwamitin sulhu ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon harin da aka kai wa sojojin gwamnatin kasar ta Lebanon.
Ban da wannan kuma, kwamitin sulhu ya jaddada cewa, zai goyi bayan gwamnatin kasar Lebanon a wannan lokaci, kana ya yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta tabbatar da gudanar da zaben shugaban kasar kamar yadda aka tsara. Sannan kwamitin sulhun ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar da su hada kai yayin da 'yan aware ke kokarin raba kan kasar, da kuma bin manufar hana tsoma baki kan rikicin kasar Syria. (Zainab)