A cikin sanarwar da kwamitin ya fitar a wannan rana ya nuna fatansa na ganin sabuwar gwamnatin Lebanon za ta kulla hulda mai ma'ana da sauran kasashen duniya, a kokarin neman samun karin goyon baya ga Lebanon tare da kungiyar ba da goyon baya ga Lebanon ta duniya.
Ban da haka, kwamitin sulhu ya jaddada cewa, gudanar da kuduri mai lamba 1701 na kwamitin sulhu na MDD da sauransu na da muhimmanci kwarai wajen tabbatar da zaman lafiya a Lebanon,don haka ya yi kira ga sabuwar gwamnatin kasar da ta tsaya tsayin daka kan demokuradiyya, musamman ma tabbatar da gudanar da babban zaben kasar bisa kundin tsarin mulkin kasar.
Haka kuma kwamitin sulhu ya yi kira ga duk 'yan kasar Lebanon da su hada kansu domin yaki da yunkurin kawo illa ga ga zaman lafiyar kasar, tare da jaddada cewa,ya kamata duk bangarori na Lebanon su cika alkawarinsu dake cikin sanarwar Babban taron, wato su dauki matsayi na 'yan ba ruwanmu, domin kauracewa sa hannu cikin rikicin Syria.(Fatima)