in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Lebanon ta yi kira ga kashen duniya da su samar da gudummawa ga sojojin ta
2014-08-27 14:59:45 cri
A jiya Talata ne shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri, ya yi kira ga kasashen duniya da su samar da gudummawa ga sojojin kasar sa, a kokarin su na inganta karfin yaki da ta'addanci. Kiran na Mr. Barri dai ya zo gabar da kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin sake tsawaita wa'adin sojojin sa dake aiki a kasar ta Lebanon.

Bisa labarin da kafofin watsa labarun kasar ta Lebanon suka bayar, an ce Barri ya gana da jakadun kasashe mambobin dindindin na kwamitin sulhun MDD dake kasar Lebanon, da kuma jami'i mai shiga tsakani na MDD dake kasar Derek Plumbly, inda ya bayyana musu cewa, kasar sa, musamman ma yankin Aarsal dake gabashi, na fuskantar barazanar 'yan ta'adda, kuma mai yiwuwa ne rikicin da ya auku a yankin na Aarsal a kwanakin baya, ya sake bulla a sauran yankunan kasar. Don haka ne ya yi kira ga kasashen duniya da su bada gudummawa ga sojojin bisa burin a hana hakan aukuwa.

A jiya Talata ne dai kwamitin sulhun na MDD ya zartas da wani kuduri na tsawaita wa'adin aikin sojojin majalisar dake kasar Lebanon shekara guda, wato har ya zuwa ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2015 mai zuwa. Kudurin ya ce, sojojin da sojojin kasar Lebanon za su taimaka wajen gina sabon yanayi a kudancin kasar Lebanon, kana ya yi kira ga sojojin bangarorin biyu, da su kara hadin gwiwa wajen sintiri da dai sauran muhimman ayyuka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China