A yayin taron, an bayyana cewa, daga farkon shekarar bana, tattalin arzikin kasar na bunkasa yadda ya kamata, sakamakon wasu matakai da aka dauka, a nan gaba kuma, ya kamata a ci gaba da inganta ayyukan yin kwaskwarima, da ci gaba da baiwa kamfanonin kasar karin ikon gudanar da ayyukansu da dai sauransu.
Bugu da kari, za a habaka ayyukan bude kofa ga kasashen waje, domin nuna goyon baya kan aikin kyautata yanayin tattalin arzikin kasar. Kana, ya kamata a ci gaba da kyautata yanayin cinikin ketare, da kuma daina matsa lamba ga kamfanonin ketare, ta yadda za a raya tattalin arzikin kasar. (Maryam)