A yammacin jiya ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Faransa François Holland a birnin Paris dake kasar Faransa .
Da farko, Li Keqiang ya mika wa shugaba Hollande sakon gaisuwa daga takwaransa na kasar Sin. Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin da Faransa sun yi imani da juna a fannin siyasa, sun kuma samu nasarori kan hadin gwiwar samun moriyar juna a tsakaninsu, kuma an sada zumunta a tsakanin al'ummomin kasashen biyu.
Kasar Sin tana son kara yin mu'amala a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu don kara yin imani da juna, da sa kaimi ga kyautata hadin gwiwarsu, da taimakawa juna wajen samun bunkasuwa, da kara hada kai a fannonin kiyaye zaman lafiya da tsaro da bunkasuwa a duniya.
A nasa jawabin, shugaba Hollande ya yi maraba da ziyarar da Li Keqiang ya kawo kasar Faransa, kuma ya bayyana cewa, dangantakar abokantaka da ke tsakanin Faransa da Sin ta shiga sabon yanayi, wadda za ta kara kawo moriya ga kasashen biyu da kuma jama'arsu.
Kasar Faransa ta yabawa gwamnatin kasar Sin bisa ga sanarwar da ta sanar wajen gabatar da takardar karfafa tinkarar sauyin yanayi nata, wannan wani muhimmin goyon baya ne da kasar Sin ta nuna wajen cimma nasarar taron sauyin yanayi na birnin Paris, kana wata muhimmiyar dama ce ga kasashen duniya wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa.
Daga bisani bangarorin biyu sun tattauna kan yadda za su fara yin hadin gwiwa a wasu bangarori guda uku, inda suka amince da kafa asusun hadin gwiwa na Sin da Faransa da nufin goyon bayan zuba jari kan sana'o'ia tsakaninsu da wani bangare na uku, da kuma sauran batutuwan hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa.
Ban da wannan kuma, Li Keqiang ya gana da shugaban majalisar dattijai ta kasar Faransa Gerard Larche da shugaban majalisar wakilai ta kasar Claude Bartolone a safiyar ranar 30 ga watan Yuni, kana ya yi shawarwari tare da firaministan kasar Faransa Manuel Valls a fadarsa dake birnin Paris a yammacin wannan rana. (Zainab)