A cikin hirar tasu, mista Medvedev ya yaba wa dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin. Ya kuma bayyana cewa yana fatan za a samu kyakkyawan sakamako a yayin taron ganawa karo na 20 tsakanin firaministocin kasashen Rasha da Sin da aka tabbatar da za a shirya kafin shekarar bana.
A nasa bangaren, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasashen Sin da Rasha kasashe makwabta ne mafi girma. Tsarin yin taron ganawa tsakanin firaministocin kasashen biyu a kullum yana da amfani. Bangaren Sin yana son hada kai da bangaren Rasha wajen shirya wannan taron ganawa mai zuwa, ta yadda za a iya samun sabon ci gaban dangantaka da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu. (Sanusi Chen)