Li Keqiang ya yi jawabi cewa, ba a samu karfi wajen farfado da tattalin arzikin duniya ba, fadada bukatun kasuwa ta hanyar bunkasa tattalin arziki shi ne hanya mafi kyau wajen tinkarar matsin lamba na raguwar tattalin arziki. Ana bukatar da kasashe masu tasowa da su kara gina ayyukan more rayuwa. Kasar Sin tana da kayayyaki masu matsakaicin inganci da na'urorin samar da kayayyakin, wadanda suka dace da bukatun kasashe maso tasowa. Kasashe masu ci gaban tattalin arziki suna da fasahohi na na'u'rori masu zamani. Kamata ya yi a hada fifikon kasashe masu tasowa da na kasashe masu ci gaba, don samar da kayayyaki masu inganci kuma masu araha ga kasashe masu tasowa, ta haka ne za a sa kaimi ga inganta sha'anin kasar Sin da fadada fitar da kayayyaki daga kasashe masu ci gaba. Hakazalika kuma, kasashen biyu suna son yin amfani da hanyoyi daban daban wajen yin hadin gwiwar su a fannonin samar da wutar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya, da jiragen kasa mafi sauri da dai sauransu domin samun moriyar juna.
A nasa bangare, Valls ya bayyana cewa, Faransa tana nuna goyon baya ga kamfanonin kasashen biyu da su yi hadin gwiwa a fannonin makamashi, kiyaye yanayi, ayyukan more rayuwa da sauransu. (Zainab)