Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana aniyar kasar sa ta rage yawan hayaki mai gurbata muhalli da take fitarwa. Mr. Li wanda ya bayyana hakan a ranar Talata a birnin Paris, ya ce kasar sa ta tsara wani kundi game da wannan manufa, ta kuma mika shi ga ofishin MDD mai kula da sauyin yanayi.
Cikin matakan da Sin din ta amince ta dauka bisa radin kan ta, hadda rage fidda hayaki nau'in CO2 a kan ko wane ma'aunin GDP da kaso 60 zuwa 65 bisa dari nan da shekarar 2030 ko ma a wani lokaci kafin wannan shekara, daga matsayin hayakin da kasar ta fitar a shekara ta 2005.