in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 12 sun mutu a sakamakon hare-haren boma-bomai a kasar Afghanistan
2015-07-13 10:45:41 cri

Jiya Lahadi, kafofin watsa labaru sun ba da labarin cewa, an kai hare-haren boma-bomai a gefen hanya sau biyu a gabashi da kuma arewacin kasar, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, a yayin da mutane 8 suka ji rauni.

Wani 'dan sandan jihar Kapisa dake gabashin kasar Afghanistan ya ce, wata mota dake dauke da fararen hula ta take boma-boman da aka dasa a gefen hanya a jiya Lahadi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10, a yayin da mutane biyu suka ji rauni. A wannan rana kuma, an kai harin boma-bomai kan wata motar 'yan sanda a gefen hanya a jihar Kunduz dake arewacin kasar Afghanistan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula biyu, a yayin da 'yan sanda biyu da wasu fararen hula 4 suka ji rauni.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai hare-haren, 'yan sanda sun riga sun fara bincike kan wadannan hare hare.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China