A kalla mutane 45 ne suka mutu yayin da wasu 60 suka jikkata a ranar Lahadi da yamma bayan wani harin kunar bakin waken da aka kai wani filin wasan kwallon raga a garin Yahya Khel, dake gundumar Paktika dake gabashin kasar Afghanistan, a cewar hukumomin kasar.
Shugaban Afghanistan Mohammad Ashraf Ghani ya yi allawadai da babbar murya da wannan harin kunar bakin wake, wanda ya kashe fararen hula 45 da ba su ji ba su gani ba, tare kuma da jikkata wasu 60, in ji fadar shugaban kasar Afghanistan a cikin wata sanarwa.
Fashewar ta faru ne a lokacin wasan kwallon raga, a cewar sanarwar. Shugaba Ashraf Ghani ya ba da umurni ga hukumomin da abin ya shafa da su samar da jinya yadda ya kamata ga wanda suka ji rauni a wannan gundumar dake kan iyaka da Pakistan, in ji sanarwar. (Maman Ada)