Shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya ba da sanarwa a ranar Talata cewa, yana hangen tsugunnar da sojojin Amurka 9800 a kasar Afghanistan har wuce shekarar 2014.
Yawan sojojin zai ragu da rabin kashi kafin karshen shekarar 2015, kuma ma'aikatan diplomasiyya na ofishin jakadancin Amurka dake birnin Kabul za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata kafin karshen shekarar 2016, in ji mista Obama a fadar White House.
Bayan shekarar 2014, in ji Obama, sojojin Amurka dake Afghanistan za su gudanar da kebabbun ayyuka biyu da suka shafi horar da sojojin kasar Afghanistan da kuma tallafawa ayyukan yaki da ta'addanci kan kungiyar Al-Qaida.
Cigaban zaman sojojin Amurka na da nasaba da yarjejeniyar dangantakar tsaro (ABS) tare da gwamnatin Afghanistan, in ji Obama.
A tuna cewa, shugaban kasar Afghanistan mai barin gado, Hamid Karzai ya ki amincewa da sake sanya hannu kan wannan yarjejeniya. (Maman Ada)