Shugaban hukumar zabe na Afghanistan, Mohammad Yusuf Nuristani, ya bayyana wa manema labarai a ranar Lahadi cewar, 'dan takarar shugaban kasa Abdullah Abdullah shi ke kan gaba, a zaben shugaban kasar da kashi 49.75 bisa dari na kuri'un da aka rigaya aka ilga.
Shugaban hukumar zaben ya ce, Abdullah, wanda tsohon ministan harkokin wajen kasar Afghanistan ne, yana kan gaba da kashi 44.4 na kuri'un da aka kada, A bayansa kuma, akwai Ashraf Ghani Ahmadzai wanda ya zo na biyu da kuri'u 33.2 bisa dari, na ukku shi ne Zalmai Rassoul da ya samu kuri'u kashi 10.4 bisa dari na kuri'un da aka jefa.
Nuristani ya ce, an yi amfani da kashi 49.75 na kuri'un da aka kada daga yankuna 34, domin samar da sakamakon farko na zaben, kamar yadda dokokin zaben suka tanadar, dole ne 'dan takara ya samu fiye da kashi 50 bisa dari na kuri'un da aka kada, kafin ya samu kaiwa ga cikakkiyar nasara. A fili take cewa dai, ana sa rai za'a gudanar da zabe tsakanin 'dan takara na farko da na biyu domin a tantance mai nasara daga cikin su.
Shugaban hukumar zaben ya ce, sakamakon zaben da aka bayyana a ranar Lahadi, wani kashi kadan ne na zaben, a inda ya kara cewar, hukumar za ta yi iyakacin kokari domin ta bayyana sakamakon zaben na farko a ranar Alhamis. Ya kuma ce, sakamakon zaben ka iya canzawa. (Suwaiba)